﻿Zabura.
122.
Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.” 
Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima. 
An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda. 
A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila. 
A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda. 
Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya. 
Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.” 
Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.” 
Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki. 
