﻿Zabura.
117.
Yabi Ubangiji, dukanku al’umma; ku ɗaukaka shi, dukanku mutane. 
Gama ƙaunarsa da girma take gare mu, amincin Ubangiji kuma madawwami ne har abada. Yabi Ubangiji. 
