﻿Zabura.
96.
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka. 
Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana. 
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane. 
Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. 
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai. 
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa. 
Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi. 
Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa. 
Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya. 
Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya. 
Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa; 
bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki; 
za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa. 
