﻿Zabura.
81.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub! 
Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi. 
Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu; 
wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub. 
Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba. 
Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an ’yantar da hannuwansu daga kwando. 
Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. Sela 
“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila! 
Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba. 
Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi. 
“Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba. 
Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu. 
“A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina, 
da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu! 
Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada. 
Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.” 
