﻿Zabura.
63.
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. 
Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. 
Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. 
Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. 
Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. 
A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. 
Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. 
Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni. 
Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya. 
Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji. 
Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata. 
