﻿Zabura.
47.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki. 
Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! 
Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. 
Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela 
Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. 
Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. 
Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. 
Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki. 
Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai. 
