﻿Ezra.
2.
Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu. 
Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana). Ga jerin mazan mutanen Isra’ila. 
Zuriyar Farosh mutum 2,172 
ta Shefatiya 372 
ta Ara 775 
ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812 
ta Elam 1,254 
ta Zattu 945 
ta Zakkai 760 
ta Bani 642 
ta Bebai 623 
ta Azgad 1,222 
ta Adonikam 666 
ta Bigwai 2,056 
ta Adin 454 
ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98 
ta Bezai 323 
ta Yora 112 
ta Hashum 223 
ta Gibbar 95. 
Mutanen Betlehem 123 
na Netofa 56 
na Anatot 128 
na Azmawet 42 
na Kiriyat Yeyarim, da Kefira Beyerot 743 
na Rama da Geba 621 
na Mikmash 122 
na Betel da Ai 223 
na Nebo 52 
na Magbish 156 
na ɗayan Elam ɗin 1,254 
na Harim 320 
na Lod, da Hadid da Ono 725 
na Yeriko 345 
na Sena’a 3,630. 
Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973 
ta Immer 1,052 
ta Fashhur 1,247 
ta Harim 1,017. 
Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74. 
Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128. 
Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139. 
Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot, 
Keros, Siyaha, Fadon, 
Lebana, Hagaba, Akkub, 
Hagab, Shamlai, Hanan, 
Giddel, Gahar, Reyahiya, 
Rezin, Nekoda, Gazzam, 
Uzza, Faseya, Besai, 
Asna, Meyunawa, Nefussiyawa, 
Bakbuk, Hakufa, Harhur, 
Bazlut, Mehida, Harsha, 
Barkos, Sisera, Tema, 
Neziya da Hatifa. 
Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda, 
Ya’ala, Darkon, Giddel, 
Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami. 
Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392. 
Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba. 
’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652. 
Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna). 
Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne. 
Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna. 
Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, 
ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200. 
Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245, 
raƙuma 435, da jakuna 6,720. 
Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake. 
Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100. 
Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu. 
